Dangote Ya Ba Mata Masu Sana’o’i Gudummawar Naira Miliyan 250 A Neja — Leadership Hausa Newspapers

0
243


Shahararren attajirin nan na Afirka Alhaji Aliko Dangote ya bayar da gudummawar zunzurutun kudi Naira miliyan 250, ga mata masu sana’o’i a jihar Neja domin taimaka musu kan sana’o’in nasu. Matan da suka samun wannan gudummawar dai sun kai su  25, 000 domin su fara gudanar da kananan sana’o’insu.

Su dai wadannan kudade gidauniyar tallafawa al’umma ce ta Aliko Dangote ke rabawa ga talakawa musamman mata domin ba su gudummawa kan yadda za su dogara da kansu ta hanyar sana’a. Gidauniyar za ta bayar da irin wannan tallafin kudin ga mata 1,000 a kowace karamar hukuma daga cikin kananan hukumomi 774 da ake da su a fadin  kasar nan.

Attajirin ya ce, ya fara  bayar da irin wannan tallafin ne tun daga shekara ta 2012, musamman domin ya tallafa wa gwamnaticin jihohi wajen bunksa tattalin arzikin mutanensu na raba al’umma da talauci.

“Manufar wannan shiri  shi ne a tallafa wa masu kananan sana’o’i yadda za su samu cim ma wasu bukatu na rayuwarsu” in ji shi.



Read More…..Leadership Newspaper