Kotu Ta Daure Tsohon Gwamnan Filato Jang A Gidan Yari — Leadership Hausa Newspapers

0
232


Tsohon Gwamnan Jihar Filato Jonah Dabid Jang a shekaran jiya ne ya ci gaba da kasancewa a gidan wakafi, biyo bayan kin amincewa da bayar da belinsa da Alkalin babban kotun Jos Justice Daniel Longji ya yi.

Jang zai ci gaba da kasancewa a gidan yarin har zuwa ranar 24 ga watan Mayun nan da muke ciki.

Jonah Dabid Jang an gurfanar da shi ne a gaban kotu kan laifuka dai-dai har guda 12 da ake zargisa da aikatawa wadanda dukkaninsu sun shafi cin hanci da rashawa na tsabar kudi har Biliyan N6.3 wadanda ya karkatar da su zuwa lalitarsa daf da barinsa ofis a matsayin gwamnan jihar.

A cikin tuhumar, an kuma hada da jami’in da ke kula da hidimar fitar da kudi na ofishin Sakataren gwamnatin jihar Filato Yusuf Gyang Pam, a bisa zargisa shi ma da wawushe naira miliyan N11.

Haka kuma, lauyan kariya na tsohon gwamnan, Barista Robert Clarke, ya rubuta bukatar bayar da belin Jang a ranar Litinin.

Clarke ya bayyana cewar Jang ya kamata ya samu ‘yanci domin a samu zarafin gudanar da bincike, ya…



Read More…..Leadership Newspaper