A Da Malam Hausa Sun Banzantar Da Marubuta Hausa Ne-Farfesa Abdalla — Leadership Hausa Newspapers

0
81


A makon jiya mun tsaya inda FARFESA ABDALLA ya ke shaida wa Editan LEADERSHIP A YAU LAHADI, NASIR S. GWANGWAZO, yadda a ka yi ya samu damar gabatar da makala a wata jami’a da ke kasar Jamus, lamarin da ya fara bude ma sa hanyar da ta kai shi ga zama farfesa a karo na biyu. Ga yadda su ka dora a zantawar:

A ka ba ni tikiti na tafi Jamani na je na gabatar da ita (makalar). To, kafin na taho sai da ita matar ta ce ka taho mi ni da litattafan soyayya na Hausar nan. Na je na jido su da yawa, na yi kwali guda na je na kai. Bayan na gama gabatar da takardar na ce ga litattafai da ki ka ce na taho mi ki da su na kawo. Sai ta ce, ‘nawa ne?’ Sai na ce ‘me ki ke nufi nawa ne? Ai ni kyauta na kawo mi ki.’ Sai ta ce, a’a, ai su na da ‘budget’ na sayen litattafan, sun rasa wanda zai je ya zakulo mu su litattafan ne. tunda ya ke yanzu na zo da su, za su kirga su, sai su biya ni kudin, kuma haka a ka yi. Ni ban yi tsammanin za su biya ni ba, amma dai a ka biya ni da wasu kudade…Read More…..Leadership Newspaper