Assasa Zaurukan Sulhu A Bauchi Ya Taimaka Wajen Gyaran Tarbiyya – Adamu Ningi — Leadership Hausa Newspapers

0
238


An bayyana assasa zaurukan sulhu don magance kalubalen da ake fiskata game da matsalar lalacewar tarbiyyar mutane a unguwanni a matsayin babbar hanyar da take tallafawa wajen rage rigingimu a tsakanin jama’a tare da rage ziyartar kotuna ko ofisoshin ‘yan sanda a lokacin da aka samu rashin jituwa a tsakanin jama’a.

Alhaji Adamu Hashimu Ningi Sakataren Zauren sulhu da tarbiyyar al’umma na unguwar ma’aikatan jinya da ma’aikatan hukumar ruwa da na ma’aikatar ayyuka da ke Bauchi shi ne ya bayyana haka cikin hirar sa da wakilin mu a Bauchi inda ya kara da cewa; sun kai shekara biyu suna kokari don assasa zauren sulhu saboda inganta rayuwar su da ta yaran su da ta jikoki da kanne kamar yadda sauran unguwanni suka yi, saboda sun jima suna wani abu kamar don ganin an samu ci gaban tarbiyya a unguwannin. Musamman ganin yadda ake ciki a yanzu wasu za su iya ganin an yi haka don a kuntata musu don an ce gyara kayanka bai zamo sauke mu raba ba. Amma idan aka jima kowa zai ga…



Read More…..Leadership Newspaper