Forestry Research Institute Ta Shirya Taron Kara Wa Juna Sani A Zariya — Leadership Hausa Newspapers

0
32


A cikin makon da gabata ne hukumar Forestry research institute of Nigeria ta shirya taron karwa juna sani ga manoma a bubban dakin taro dake cibiyar nazarin aikin gona dake jami’ar Ahmad Bello Zariya (I.R.A).

A farkon taron an sami halartar manyan baki daga cibiyoyin nazarin aikin gona da masana a bangaren ilmin gandun daji da sarakuna da shugabanin kungiyoyin manoma na bangarori da dama bubban bako a wannan waje shine minisata muhalli na kasa Alhaji Ibrahim Usman Jibril sai wakilin shugaban jami’ar ABU daya rufa mashi baya a wajan bude wannan taro.

Taron dai an shiryashine don baiwa manoma ilmin sabbin dabarun aikin noma da raya itatuwa a fadin kasa baki daya don samun mafita ga canjin yanayi da ake samu a halin yazu.

Alhaji Bawa ’Yargada Sarkin Noman Gundumar Rigasa Kaduna da Buhari Lawal dukkansu mahalatta taronne sun shaida jaridar Leadership A yau cewa, tabbas sunyi farin ciki da wannan taro domin suna samun dabarun noma Wanda da hakan na amfanar da kasa baki daya…Read More…..Leadership Newspaper