Shugaban Karamar Hukuma Ya Cire Hakorin Kwamishiniya A Adamawa — Leadership Hausa Newspapers

0
217


Kwamishiniyar ma’aikatar albarkatun kasa ta jihar Adamawa Misis Shanti Sashi, ta maka shugaban karamar hukumar Lamurde Mista Barati Nzonzo a kotu, biyo bayan marin da ya wanka mata wanda ya yi sanadin cire mata hakori.
Misis Sashi, ta maka shugaban karamar hukumar Lamurde a kotu ne kan batutuwa bakwai da suka shafi aikata munanan laifuka, ta kuma zargi shugaban da ci mata mutunci da azaba mai tsanani, da ya kai ta ga rasa hakora
To sai dai lokacin da aka kira shari’ar gaban wata kotun majistare a ranar juma’ar da ta gabata a Yola, wanda ake zargin ya ki halartar zaman kotun.
Lauyar dake tsaya wa wacce ta kawo kara, Misis Mfoniso Gabriel, ta bukaci kotun da ta yi amfani da sashi na 154 karamin sashi na 1, na kundin tsarin dokar masu aikata miyagun ayyuka (CPC) ta bada umurnin kamo wanda ake zargin.
Shi kuwa Mista Jerry Ifegwu, lauya da ke kare wanda ake zargin ya ce, batun amfani da wacce dokar bai taso ba, domin wanda yake karewa bai bayyana a kotun ba.
Ya ce duk da wanda yake…



Read More…..Leadership Newspaper