Kallo Ya Koma Sama Bayan Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus — Leadership Hausa Newspapers

0
262


A Larabar nan ne aka samu wata wasikar da mataimakin gwamnan jihar Bauchi Injiniya Nuhu Gidado ya aike wa gwamnan jihar Bauchi, Muhammad Abdullahi Abubakar, yana shaida masa ajiye mukaminsa na mataimakin gwamnan nan take.

Tsohon mataimakin gwamnan ya bayyana cewar ya kamata ne ya kasance har karshen wannan wa’adin, amma a sakamakon wasu dalilai ya yanke shawarar sauka daga matsayin nasa.

Ya bayyana cewar, ci gaba da kasancewarsa a ofishin hakan tamkar rashin yi wa kansa adalci ne, don haka ne ya zabi barin ofishin.

Gidado ya ci gaba da cewa tun a ranar 19, ga watan Afirilun 2018, ne ya fara tunanin ajiye wannan matsayi.

Gidado ya gode wa gwamna Abubakar da kuma jama’ar jihar Bauchi  bisa ba shi dama a matsayin mataimakin gwamnan jihar na tsawon lokaci.

Tun da fari, Nuhu Gidado ya fara ne da nuna godiyarsa  bisa yadda gwamnan jihar Bauchi ya ba shi damar zama mataimakinsa na tsawon lokaci, ya yi bayanin cewar ya kammala yanke shawararce a kashin kansa domin fuskantar wata…



Read More…..Leadership Newspaper