Masarautar Isa A Sakkwato Ta Tara Kudin Zakka Naira Milyan Shida — Leadership Hausa Newspapers

0
261


A hobbasar kwazonta na karba da kuma rarraba zakka ga wadanda suka cancanta, Masarautar Isa a karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Gobir na Isa, Mai Girma Alhaji Nasiru Usman Ahmad II ta samu nasarar tara kudin zakka da wakafi wadanda adadinsu ya kama naira miliyan shida.

Mai Girma Sarkin Gobir na Isa ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a fadarsa a yayin da yake bayani a wajen rarraba zakka da Gundumar Isa ta tara a kwarya-kwaryar bukin wanda Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar ya jagoranta.

Haka ma Sarkin Gobir na Isa ya bayyana cewar Masarautarsa a Karamar Hukumar Isa da ke Jihar Sakkwato ta tara buhun shinkafa 200 da shanu 16 da kuma tumaki da awaki 56.

“Masarautar Isa ta samu nasarar karbar gonaki uku a matsayin wakafi wadanda daga cikin su akwai gona mai hekta 10 da kuma mai hekta 3. Mun kuma samu wakafin fili wanda kudinsa ya kai naira milyan 2, 950 wanda akalla mutane 750 za su amfana.” In ji Sarkin.

A jawabinsa Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji…



Read More…..Leadership Newspaper